10 Afirilu 2026 - 22:25
Source: ABNA24
Hizbullah Na Ci Gaba Da Ruwan Wuta Akan Isra’ila Da Sojojinta

Hizbullah ta sake kai wa garin Avium hari da makamai masu linzami wanda ya ke matsugunan sahayoniya ne a arewacin Falasdinu a matsayin martani ga munanan laifukan da gwamnatin ta'addanci ta Isra'ila ke yi wa al'ummar Lebanon.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sannan Hizbullah ta kai wa garin Muskaf harida makami mai linzami wanda wannan shi ne hari karo na uku da Hizbullah ta kai wannan garin na Maskaf. Hizbullah ta kasar Lebanon ta harba rokoki kan matsugunan sahyoniyawa garin Al-Malikiyya da ke arewacin Falasdinu. Sannan Hizbullah ta harba rokoki a yankunan Naharia a matsayin martani ga munanan hare-haren da gwamnatin Sahayoniya ke yi da kuma keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

Hizbullah ta kasar Lebanon ta fada a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, a yau ne mayakan gwagwarmayar Islama suka kai hari kan motar Hommer sojojin Isra'ila a garin Taiba da ke kan iyaka da wani jirgin kunar bakin wake tare da haifar da asarar rai da rauni. Hizbullah na ci gaba da kai hare-haren makami mai linzami na kan wuraren sahyoniyawa da ke arewa maso yammacin kasar Falasdinu’ sannan ta kai hari kan garin Safad da aka mamaye. Sannan ta kai harin makami mai linzami a Stila Maris mallakar sojojin Isra'ila a birnin Haifa. Hizbullah ta kai hari kan garin Naharia na Sahayoniya a matsayin martani ga karya yarjejeniyar tsagaita wuta.

A wasu rahotannin Hizbullah ta fara kai harin makami mai linzami daga kudancin Lebanon zuwa arewa in da ta kai hari kan sansanin Sharaga, hedkwatar gudanarwa ta Gulani na sojojin Isra'ila a arewacin birnin Akka da aka mamaye da makamai masu linzami da jirage marasa matuka. Hizbullah ta kai hari kan sansanin Kariat Shamuneh da sansanin Bait Hill. Kuma ta hari kan wuraren sojojin sahyoniyawa da motocinsu a kusa da makarantar Al-Ishraq da ke birnin Bint Jbeil da makamai masu linzami guda biyu. Ta kuma kai hari ga Garrison na Kariat Shemmoneh da sansanin Bait Hell da jirage marasa matuka, Sannan ta kai hari kan ababen more rayuwa na sojojin Isra'ila a garin Karmil na Sahayoniya a karo na biyu a matsayin martani ga harin da abokan gaba suka yi a birnin Suor da makamai masu linzami. Kafofin yada labarai na Hebrew sun ba da rahoton cewa, biyo bayan harin makami mai linzami na kungiyar Hizbullah, an ji karar fashewar wani abu a garin Kariat Shamuneh ba tare da kunna ƙararrawar gargadi ba. Ta kuma kara atbbatar da cewa za ta ci gaba da mayar da martani har sai Isra'ila tadakatar dakai hari kan kasar Labanon da mutanenta.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha